Me ka ke nema?


Shafin Farko

Fadar Gwamnatin Najeriya


Gabatarwa

Fadar Ƙasa ita ce fadar Gwamnatin Tarayya wadda ake kira State House a Turance. Wannan fada, ayari ne na ofisoshi da suka haɗa da Fadar Shugaban Ƙasa wadda ake kira Presidential Villa a Turance; ofishin mataimakin shugaban ƙasa, da sauransu.

Haka nan kuma a cikin fadar ta shugaban ƙasa akwai ma’aikatan da suke gudanar da ayyukan da suka shafi ayyukan gudanarwa, tsare-tsare bisa ƙa’ida, harkar tsaron lafiyar shugaban ƙasa da fadar tasa da kuma harkokin yaɗa labarai, waɗanda dukkan su suke ƙarƙashin kulawar shugaban ma’aikatan gidan Gwamnatin Tarayya, wato Chief of Staff kenan a Turance, muƙamin da a yanzu haka (2019), Abba Kyari yake riƙe da shi. 

Manufar wannan rubutu da mai karatu yake karantawa ita ce yin cikakke kuma gamsasshen bayani game da wannan fada ta Gwamnatin Tarayyar Jamhuriyar Najeriya. Abin yi kawai shi ne a riƙa bibiyar wannan shafi sannu a hankali kasancewar za a riƙa sabunta shi a duk lokacin da aka samu wani sabon bayani.

Bila

Bila, wadda ake rubutata ta da Villa a Turance, suna ne na fadar Shugaban Ƙasar Najeriya, wadda kuma jerereniya ce ko na ce ayari ne na gine-gine wanda ya haɗa da ofishin Shugaban Ƙasar Najeriya; gidan kwanansa tare kuma da sauran ma’aikatan da ke da alaƙa da shi kai tsaye da sauransu.

Tarihi

Tun cikin shekarar 1976 gwamnatin soja ta Janar Murtala Mohammed GCFR mai rasuwa, ta yanke hukuncin canja matsugunnin babban birinin Tarayyar Jamhuriyar Najeriya daga Lagos, zuwa wani guri mafi zama tsakiyar ƙasa wanda ta kafa kwamatin da Justice Akinola Aguda ya jagoranta domin bayar da shawarwari. Wannan kwamati na Aguda ya bayar da shawarar kafa Babbar Cibiyar Gwamnatin Tarayya  Federal Capital Territory (FCT) a tsakiyar ƙasa. Sakamakon wannan, sai Janar Murtala Mohammed GCFR ya yi wa ‘yan ƙasa bayani a ranar 3 ga watan Faburairu na shekarar 1976.

Tun daga wancan lokaci ake ta shirye-shirye har zuwa farkon shekarun 1980, a zamanin zaɓaɓɓiyar gwamnatin farar hula ta Alhaji Shehu Shagari, GCFR aka fara gina wannan katafariyar cibiyar gwamnatin Tarayyar Najeriya a Hukumance; abin da ya saka ake yi wa shi marigayi Alhaji Shehu Shagari GCFR kallon wanda ya fara gina Abuja a matsayin Babbar Cibiyar Gwamnatin Tarayyar Najeriya.

Ginin da aka sakawa suna Gidan Akinola Aguda; wato Akinola Aguda House a Turance, ya zama Matsugunnin Shugaban Ƙasa da kuma Masaukin Baƙin Shugaban Ƙasa wanda aka buɗe shi a hukumance a ranar 1 ga watan Oktoba na shekarar 1983. Ginin ya ƙunshi gidan Shugaban Ƙasa na wucin-gadi a hukumance (Kafin a gina masa na dindindin), da kuma Gidajen Baƙi waɗanda Shugabannin wasu ƙasashen za su iya zama a ciki a lokutan ziyarar aiki a zamanin shugabancin Alhaji Shehu Shagari GCFR.

A cikin watan Oktoba na shekarar 1983, Gidan Aguda ya karɓi baƙuncin zaman tattaunawar Majalisar Ministoci na farko da aka taɓa yi a wajen garin Lagos, wasu ‘yan kwanaki kaɗan bayan Abuja ta karɓi baƙuncin taron Taya Murnar Samun ‘Yancin Kan Ƙasa a karon farko.

Daga ƙarshe, Shugaba Ibrahim Babangida GCFR, wanda ya karɓi mulki a shekarar 1985, ya bayar da umarnin ƙara gina wasu sababbin gidajen shugaban ƙasa, wanda aka kammala gina rukunin gidajen shugaban ƙasa da ke Dutsen Aso a shekarar 1991, wanda kuma, shi shugaba Ibrahim Badamasi Babangida GCFR ya zama shugaban ƙasa na farko da ya tare a wannan gida a ranar 12 ga watan Disamba na shekarar 1991.

Bayan kammala gina sababbin rukunin gidajen da suka zama sabuwar faduwar shugaban ƙasa, sai aka mayar da wancan tsohon ayarin gine-gine, wato Gidan Aguda, zuwa fadar Mataimakin Shugaban Ƙasa, wanda kuma har zuwa yau ɗin nan (2019), haka abin yake kamar yadda aka wallafa a shafin Intanet na Gwamnatin Tarayyar Jamhuriyar Najeriya, duk kuwa da cewa, Mataimakin Shugaban Ƙasa ya taɓa zama a ayarin gidajen da aka ware wa babban jojin Najeriya daga shekarar 1999 zuwa 2007, wato a taƙaice dai, Atiku Abubakar GCON shi ne wanda ya yi wannan zama, a zamanin gwamnatin Janar (Ritaya), Obasanjo GCFR.
Sakamakon haka, gwamnatin shugaba Goodluck Ebele Jonathan GCFR ta ƙaddamar da gina wani sabon gidan Mataimakin Shugaban Ƙasa a shekarar 2010, duk da cewa, bayan ɗarewar shugaban ƙasa Muhammad Buhari GCFR aikin ya tsaya bisa hujjar cewa, akwai wasu ayyukan da suka fi yin ginin muhimmanci. A ta wannan dalilin, har zuwa lokacin yin wannan rubutun (2019), Mataimakin Shugaban Ƙasa, Osinbajo GCON, yana nan zaune cikin gidan Aguda da ke fadar ta shugaba Ƙasa (State House, 2018).

Yadda Fadar Take

Wannan fada ta Gwamnatin Tarayyar Jamhuriyar Najeriya, tana tsugunne ne a Yanki na Uku na Soji a Babban Birnin Tarayyar Jamhuriyar Najeriya wanda ya ƙunshi Fadara Shugaban Ƙasa wanda shi kuma yake ƙunshe da ofishin Shugaban Ƙasa, gidan kwanan shugaban ƙasa, ofishin mataimakin shugaban ƙasa da kuma ofishin matar shugaban ƙasa; Cibiyar Zaman Tattaunawa ta Fadar Gwamnatin Tarayya, Conference Centre a Turance; ofisoshin ƙari, State House Annexe; da kuma gidan Akinola Aguda. Ita kuwa waccar tsohuwar Fadar Gwamnatin Tarayyar wadda take a Lagos, a yanzu haka an damƙa ta ga Gwamnatin Jahar Lagos a cikin shekarar 2017, kamar yadda ya zo a shafin Gwamnatin Tarayyar Jamhuriyar Najriya na shekarar 2018.

Manazarta:


Ofo N. (2009). Rethinking the Leadership Role of the Vice-President of Nigeria. Za a iya samu a SSRN: https://ssrn.com/abstract=1585218 ko http://dx.doi.org/10.2139/ssrn.1585218

Shokefun J. (2010). Administrative Law. National Open University of Nigeria. An ciro a shekarar 2019 daga shafin: http://nou.edu.ng/sites/default/files/2017-10/PUL743%20ADMINISTRATIVE%20LAW.pdf

State House (2018). The Presidency. An ciro a shekarar 2019 daga shafin: http://www.statehouse.gov.ng

WAEC (2015). Government Paper 2, Nov/Dec. 2011. An ciro a shekarar 2019 daga shafin https://waeconline.org.ng/e-learning/Government/Govt220NQ9.html

Wikipedia (2019). President of Nigeria. An ciro a shekarar 2019 daga shafin: https://en.wikipedia.org/wiki/President_of_Nigeria


Koma Babban Shafin Tarihi

Tarihin Najeriya


Shugabannin Ƙasa


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub